Home Home El-Rufa’I Ya Roki ‘Yan Kaduna Kar Su Zaɓi PDP A Shekara Ta...

El-Rufa’I Ya Roki ‘Yan Kaduna Kar Su Zaɓi PDP A Shekara Ta 2023

230
0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, ya roƙi al’ummar jihar Kaduna cewa kada su zaɓi jam’iyyar PDP a shekara ta 2023, domin a cewar sa, kada ta ƙara jefa kasar nan cikin matsalar da ta baro a baya.

Rahotanni sun ambato El-Rufa’i ya na cewa, ya kamata jama’a
su hadu baki daya domin zaɓen mutumin da zai tsaida dan
takarar gwamnan jihar a zaben shekara ta 2023, ya na mai cewa
wannan ne lokacin da ya dace ‘yan Kaduna su amince da shi da
abin da zai zaɓa wa jihar.

El-Rufa’i ya kara da cewa, ba don abin da Sanata Shehu Sani da
Sulaiman Hunkuyi su ka yi na hana Kaduna ta karbo bashi ba,
da yanzu ayyukan ci-gaba sun mamaye jihar fiye da wadanda
ake gani a halin yanzu.

A karshe ya gargadi al’ummar jihar Kaduna, cewa su bude ido
da kyau domin zaɓen abin da ya dace, wanda zai ciyar da su
gaba ba janyo masu koma-baya ba.