Home Home Cuwa-Cuwa: Majalisa Ta Gano N4.5Bn Na Aikin Barikin ‘Yan sanda A Cikin...

Cuwa-Cuwa: Majalisa Ta Gano N4.5Bn Na Aikin Barikin ‘Yan sanda A Cikin Kasafin NDLEA

106
0

Majalisar dattawa ta yi watsi da rahoton kwamitin kula da miyagun kwayoyi, cewa ya gano wasu kudi Naira Biliyan 4 da rabi da aka ware domin gina barikin ‘yan sanda a kasafin shekara ta 2022 na hukumar NDLEA.

Yayin mika rahoton, shugaban kwamitin Sanata Hezekiah
Dimka, ya ce kwamitin sa ya gano lamarin ne, bayan duba
takardun kasafin kudin da ma’aikatar kudi ta gabatar masu.

Kwamitin dubawa a karkashin shugabancin Sanata Barau Jibrin,
ya yi watsi da rahoton kasafin hukumar NDLEA, sannan ya
bukaci kwamitin da ya koma tare da gyara matsalar.

Haka kuma, Kwamitin muhalli na majalisar dattawa a karkashin
shugabancin Sanata Ike Ekweremadu, ya gano wasu kudi Naira
Biliyan 16 da aka bukata a kasafin shekara ta 2022, domin biyan
bashin da aka ciyo na aiwatar da aikin hukumar yaki da zaizayar
kasa.

Ekweremadu, ya ce bashin an yi za a fara biyan shi ne bayan
shekaru goma, kuma ya dace gwamnatocin jihohin da su ka yi
amfani da shi ne za su biya ba gwamnatin tarayya ba.