Home Labaru Kiwon Lafiya  An Gudanar Da Zanga-Zangar Kyamar Dokar Kullen Korona A Turai

 An Gudanar Da Zanga-Zangar Kyamar Dokar Kullen Korona A Turai

47
0

Kasar Belgium ta zama ƙasa ta baya bayan nan da ta fuskanci mummunar tarzomar nuna ƙin amincewa da dokar kullen korona.

Masu zanga-zangar a Brussels sun yi arangama da ƴan sanda bayan wani tattaki na fiye da mutum dubu 30.

Masu zanga-zanga sun yi arangama da jami’an tsaro inda suka dinga jifan jami’an tsaron da duwatsu, inda jamai’an tsaro suka harba musu hayaki mai sa hawaye.

Itama kasar Neitherlands ta fuskanci Rikici mafi muni a ƙarshen makon da ya gabata, sa’ilinda da masu tada hatsaniya suka mamaye birnin Rotterdam suna cinna wa ababen hawa wuta.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Dubban Mutane a kasashen  Austria da Croatia da Denmark sun bijirewa yadda aka sabunta dokar kullen koronar a ƙasashen.