Home Home Garkuwa Da Mutane: Mahara Sun Sace Kwamishina a Jihar Benuwe

Garkuwa Da Mutane: Mahara Sun Sace Kwamishina a Jihar Benuwe

26
0

Wasu mahara sun sace kwamishinan gidaje da raya karkara na jihar Benuwe, Ekpe Ogbu.

Mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin tsaro kanar Paul Hemba ya tabbatar sace kwamishinan inda yace an sace shi ne da yammacin ranar Lahadi a mahaɗar Adankari kan hanyar Otukpo-Ado.

Ya tabbatar da cewa an gano motar da kwamishinan ke ciki a lokacin sace shi, kuma tuni jami’an tsaro suka fara bincike.

Sai dai ya ce ya zuwa yanzu ba’a samu wani labari daga waɗanda suka sace shi ba.