Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna Afrika ta kudu, ta ce an sake kashe wani dan Nijeriya mai suna Tony Elechukwu, lokacin da wani dan bindiga ya dirka masa harsashi a yankin Witbank Mpumalanga.
Shugaban ‘yan Najeriya mazauna kasar Ben Okoli ya tabbatar da aukuwar lamarin, a cikin wata wasika da ya aike wa ofishin Jakadancin Nijeriya a Johannesburg.
Okoli, ya ce wannan shi ne karo na uku da ake kashe ‘yan Nijeriya a cikin wannan watan, bayan wadanda aka kashe a ranakun 6 da kuma 9 ga wannan watan.
You must log in to post a comment.