Home Labaru Damfara: An Kama Wani Mai Amfani Da Sunan El-Rufa’i Ya Na Cutar...

Damfara: An Kama Wani Mai Amfani Da Sunan El-Rufa’i Ya Na Cutar Mutane

275
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna, ta kama wani mai suna Mohammed Jamilu da ya kware wajen amfani da sunan mutane domin bata masu suna.

Wanda ake tuhumar dai ya kware wajen amfani da sunan gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya na aikata laifuka, inda ya ke tsoratar da wadanda ya ke cutar ta hanyoyi da dama.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kaduna Ahmad Abdulrahman da ya gabatar da wanda ake zargin a helkwatar ‘yan sanda ta Kaduna, ya ce wanda ake tuhumar ya na zuwa wajen malamai ya na amfani da sunan gwamnan ya na sanya fargaba da tsoro a zukatan su domin ya damfare su.

Ya ce Mohammed Jamilu dan shekaru 30 a duniya, ya rika zuwa wajen manyan mutane da malamai ya na magana da su, inda ya ke bayyana masu cewa El-Rufa’i ne ya dauke shi domin ya ga ya kawar da irin su a jihar, inda a karshe zai karbi kudi masu dimbin yawa ya gudu. Kwamishinan ya ce, Jamilu ya amsa laifinsa, kuma ya bada bayanan da za a iya amfani da su a kotu.

Leave a Reply