Rundunar ’yan Sanda ta Jihar Kaduna, ta bada sanarwar kama wasu batagari 36 a cikin ‘yan makonni kadan tare da kwato shanun da barayin shanu su ka sace har 486.
Kwamishinan ‘yan Sanda na Jihar Kaduna Ahmad Abdurrahman ya bayyana wa manema labarai haka a Kaduna, inda ya danganta nasarar da gagarumin shirin tsaro na Operation Puff Adder shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya ya ya kaddamar.
A karkashin shirin dai, an karfafa matakan tsaro a kan titin Kaduna zuwa Abuja, inda a cikin wannan shekarar garkuwa da mutane ta kara muni a kan titin.
Ya ce an kuma samu kama batagari a wurare daban-daban da ake zargi da aikata laifuffuka da dama a cikin jihar Kaduna, ya na mai cewa sun kwato shanu 393, da tumaki 93 daga hannun barayin shanu.
Daga cikin batagarin da aka kama kuwa, an samu tara da hada hannu da masu fashi da makami, da wasu 18 masu garkuwa da mutane da kuma mutane shida masu satar shanu.