Home Labaru Daga Darajar Kasa: Oni Na Ife Ya Bukaci ‘Yan Jarida Su Guji...

Daga Darajar Kasa: Oni Na Ife Ya Bukaci ‘Yan Jarida Su Guji Yada Labarai Marasa Kyau Game Da Najeriya

1209
0

Oni na Ife Oba Enitan Ogunwusi, ya bukaci kafofin yada labarai da masu yawon bude ido su rika ba da labarai da za su daga darajar Najeriya a idon duniya muhimmanci.
Ogunwusi, ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara na kungiyar masu yawon bude ido a fadarsa dake Ille Ife.
Ya ce yin hakan zai janyo hankalin masu masu zuba jari da yawon bude ido da zai janyowa Nigeria habbakar tattalin arziki, da daraja a idon duniya.
Ya ce kowacce kasa tana da matsalolin ta, amma tana bin dukkanin hanyoyin da suka kamata dan ganin bai bata mata suna a idon duniya ba.
Ya kara da cewa akwai bukatar kafofin yada labarai da masu yawon bude ido su fi maida hankali kan abubuwa dake faruwa masu kyau da za su daga darajar Najeriya.

Leave a Reply