Home Labaru Inganta Ilimi: Gwamna Jihar Beyelsa Yaba Jonathan Mukami

Inganta Ilimi: Gwamna Jihar Beyelsa Yaba Jonathan Mukami

276
0

Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya nada tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin mai bashi shawara na musamman kan harkokin ilimi.
Dickson ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da asusun inganta ilimi a Yenagoa, babban birnin jihar.
Ya ce tsohon shugaban zai maida hankali ne wajen sanya ido Kan yadda kudade ke shiga da Kuma fita a gidauniyar ta kula da ilimi.
Dickson ya Kara da cewa wannan bai rasa nasaba da irin kokarin da Jaonathan ya yi wajen yiwa ilimi kyakkyawan tanadi a lokacin da yake gwamnan jihar.
A lokacin da yake amsar aikin, Jonathan ya yi alkawarin yin iya bakin kokarinsa wajen ingantar ilimi ta yadda al’ummomin jihar za su amfana.
Sannan ya bukaci mutanen jihar da su Rika amfani da damar da suka samu wajen ilmantar da kawunansu, da kuma ‘ya’yan su.

Leave a Reply