Home Labaru Kasuwanci Bunkasa Tattalin Arziki: Shugaba Buhari Ya Bukaci Masu Hannu Da Shuni Su...

Bunkasa Tattalin Arziki: Shugaba Buhari Ya Bukaci Masu Hannu Da Shuni Su Zuba Jari A Najeriya

410
0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci masu arzikin Najeriya su rika zuba jari a cikin gida musamman bangarorin dake neman durkushewa domin ingantan tattalin arzikin kasa.
Buhari ya bukaci hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan kasuwa da kuma shugabannin jam’iyyar APC wajen bude baki a fadarsa dake Abuja.
Ya ce yin hakan zai magance wasu matsaloli da dama da Najeriya ke fuskanta da suka hada da rashin aikin yi da sauransu.
A cewarsa muhimmancin ‘yan kasuwa da shugabannin siyasa ya kai su taimaka wajen tabbatar da habakar tattalin arziki.
Sannan ya nemi hadin gwiwarsu wajen kara inganta harkoki musamman ma zuba jari a tattalin arzikin Nigeria.
Ya kuma ba bakin nasa tabbaci cewa gwamnatinsa ba za ta tsaya a iya yaki da cin hanci da rashawa, magance tsaro da kuma hana fasakwabri ba, za ta maida hankali wajen samar da yanayi mai kyau ga ‘yan kasuwa, ta yadda za su ci gaba da gudanar da harkokin kasuwancin su yadda ya kamata.

Leave a Reply