Home Labaru Kasuwanci Cunkoson Apapa: Direbobin Manyan Motoci Sun Bijire Wa Umarnin Buhari

Cunkoson Apapa: Direbobin Manyan Motoci Sun Bijire Wa Umarnin Buhari

678
0

An shiga mako na biyu kenan, tun bayan da Fadar Shugaban kasa ta bada umarnin a yi gaugawar janye manyan motocin da su ka yi dandazo a Apapa da kewaye a Lagos.

An dai bada umarnin ne tun ranar 22 Ga Mayu, tare cewa a gaggauta cire manyan tirelolin da ke ajiye a kan gadoji da titunan yankin Apapa da kewayen ta.

Sai dai wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa, har yanzu manyan motocin su nan jibge a Apapa da kewayen hanyar Tsibirin Tin Can.

Majiyar ta ce babu wani abu da ya canja tun daga unguwar Mil sha biyu har zuwa Tsibitin Tin-can.