Home Labaru Tsaro: Sojoji Sun Kama Karin Gungun Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar...

Tsaro: Sojoji Sun Kama Karin Gungun Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar Katsina

1005
0

Rundunar sojin Nijeriya, ta ce dakarun ta sun kama wani gungun masu garkuwa da mutane, da su ka addabi kauyukan da ke yankin Funtua zuwa Faskari a jihar Katsina.

Kakakin rundunar sojin Nijeriya Kanal Sagir Musa, ya ce sojoji sun kama gungun da ya kunshi mutane biyar a samamen da su ka kai a kauyukan Sheme da dajin Ruwan Godiya.

Kanal Musa ya kara da cewa, masu laifin sun amsa cewa tabbas su na da hannu a mafi akasarin sace mutane da ake yi a kauyukan yankin Funtua zuwa Faskari, inda su ke mika wadanda tsautsayi ya fada masu zuwa manyan jagororin su da ke kuryar dajin Ruwan-Godiya.

A cikin watan Mayu da ya gabata dai, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kama masu garkuwa da mutane 93 da tarin makamai, wadanda su ka addabi jama’a a jihohin Neja da Katsina da kuma Kaduna.

Leave a Reply