Home Labaru Rikicin APC: Oshiomole Bai Cancanci Shugabancin Jam’iyyar Ba – Oyegun

Rikicin APC: Oshiomole Bai Cancanci Shugabancin Jam’iyyar Ba – Oyegun

364
0

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Cif John Odigie-Oyegun, ya ce shugaban jam’iyyar na yanzu Adams Oshiomhole ba ya da kwarewar jagorancin da ake bukata.

Oyegun ya soki Oshiomhole ne a lokacin da ya ke maida martani a kan zargin da wasu jiga-jigan jam’iyyar ke yi ma sa, cewa ya na da hannu a rikicin cikin gidan da jam’iyyar APC ke fama da shi.

John Oyegun, ya ce rashin kwarewar Adams Oshiomhole ne ya tsunduma jam’iyyar a halin da ta ke ciki na matsalolin da ta ke fuskanta a wasu jihohi ciki har da Zamfara.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne, wasu daga cikin shugabannin jam’iyyar APC a yankin kudu maso kudancin Nijeriya su ka bayyana zargin cewa, Oyegun na da hannu a rikicin cikin gida da sauran matsalolin da su ke fuskanta a baya-bayan nan.

Takaddamar dai ta kunno kai ne, bayan mataimakin shugaban jam’iyyar APC reshen arewacin Nijeriya Sanata Lawal Shu’aibu ya bukaci Adams Oshiomhole ya yi murabus, saboda gazawar sa wajen karfafa jam’iyyar tun bayan zaben sa a matsayin shugaban ta.

Leave a Reply