Home Coronavirus COVID-19: Shugaba Trump Ya Yi Gargadin Karuwar Cutar Korona A Amurka

COVID-19: Shugaba Trump Ya Yi Gargadin Karuwar Cutar Korona A Amurka

100
0

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa cutar korona za ta ta’azzara kafin a samu sauƙi a ƙasar, a yayin da ya dawo da taron da yake gudanarwa kan cutar.

Trump ya kuma buƙaci dukkan Amurkawa su riƙa sanya takunkumi, Inda kara dacewa sanya shi wata alamace dake nuna kishin ƙasa.

Shugaban wanda ba ya sanye da takunkumi a lokacin jawabin, a baya ya yi watsi da batun sanya takunkumin yana mai cewa yin hakan rashin tsafta ne.

Rahotanni sun ce masu ba shi shawara ne suka matsa masa ya ɗauki matakin sakamakon ci gaba da yaɗuwar cutar a faɗin Amurka.

A cikin jawabinsa a karon farko bayan ya dakatar da yin taron a Fadar White House kan annobar ta korona, Shugaba Trump ya yi gargadi ga Amurkawa inda ya bukaci matasa su kaurace wa shiga taron jama’a.

A yayin taron an hango Trump riƙe da takunkumi a hannunsa inda ya shaida wa manema labarai cewa zai saka tare da kuma yin kira ga Amurka su dinga sakawa idan har ba za su iya bayar da tazara tsakaninsu ba.