Home Labaru Cutar Ebola: Adadin Mutanen Da Suka Kamu A Congo Ya Kai 60.

Cutar Ebola: Adadin Mutanen Da Suka Kamu A Congo Ya Kai 60.

149
0

Adadin mutanen da suka kamu da cutar Ebola a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo a baya-bayan nan, ya kai 60.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta gargadi cewa, cutar na iya bazuwa a yayin gudanar da jana’izar mutanen da ta kashe.

Kwararren Jami’in Ayyukan Gaggawa na Hukumar Lafiya ta Duniya Mike Ryan ya ce, an samu sabbin mutane uku da suka kamu da cutar ta Ebola a karshen makon da ya ganata.

kuma yanzu adadin mutane 56 aka tabbatar sun kamu da ita, yayin da wasu mutum hudu suka fara nuna alamun kamuwa da cutar a kasar ta Congo.

A yayin zantawa ta kafar bidiyo daga shalkwatan Hukumar Lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Geneva, Mista Ryan ya ce, har yanzu wannan cuta na yaduwa ba tare an shawo kanta ba, yana mai nuna damuwa kan yadda jana’izar mamatan ke barazana ga al’ummar kasar.

Wannan dai shine karo na 11 da cutar ke barkewa a kasar Congo tun lokacin da aka fara gano ta a shekarar 1976, inda a ‘yan shekarun baya-bayan nan ta hallaka mutane fiye da dubu 2 a kasar.

Cutar ta sake bulla ne a kasar ta Congo  a dai dai lokacin da masu dauke da cutar Covid-19 ya zarta dubu 8.