Home Labaru Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Sauke Hafsoshin Tsaron Nijeriya

Tsaro: Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Sauke Hafsoshin Tsaron Nijeriya

224
0

Majalisar Dattawa ta bukaci manyan hafsoshin tsaron Nijeriya su ajiye muƙaman su, a daidai lokacin da ake ci-gaba da fuskantar matsalolin tsaro a Nijeriya.

Sai dai Shugaba Muhammadu Buhari ya gwale ‘yan majalisar, inda ya ki amincewa da kiran da su ka yi na ya sauke manyan hafsoshin tsaron Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta wallafa a shafin ta na Twitter, ta ce nadawa da sauke hafsoshin tsaron ya na hannun shugaban kasa ne, don haka shi kadai ne zai yanke hukunci a kan makomar su.

Ta ce majalisar dattawa ta amince da kudurin da ya yi kira ga hafsoshin tsaro su sauka daga mukaman su ko kuma a cire su saboda tabarbarewar tsaron kasar nan.

Sanarwar ta cigaba da cewa, Fadar shugaban kasa ta yi duba ga wannan kuduri, kuma ta na jaddada cewa nadawa da cire hafsoshin tsaro alhakin shugaban kasa ne, kuma Shugaba Buhari a matsayin sa na Kwamadan rundunar sojin Nijeriya zai yi abin da ya fi ma kasar nan alfanu