Home Coronavirus Covid-19: Karin Mutum 790 Sun Kamu Da Korona a Najeriya

Covid-19: Karin Mutum 790 Sun Kamu Da Korona a Najeriya

66
0
COVID-19: Karin Mutum 4 Sun Kamu A Najeriya
COVID-19: Karin Mutum 4 Sun Kamu A Najeriya

Hukumar daƙile yaduwar cutuka ta kasa NCDC, ta ce an samu Karin mutum 790 da suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar.

Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu sun fito ne daga Jihar Legas, inda aka samu karin mutum 574 dauke da cutar.

Sai kuma Jihar Rivers da aka samu Karin mutum 83, sai Ondo mutum 38 da kuma Ogun mutum 31.

Hukumar tace a Jihar Oyo ma an samu mutum 23, Delta mutum 10 da kuma Abuja mai mutum 9.

Sauran jihohin da aka samu masu ɗauke da cutar sun haɗa da Ekiti mutum 7 da Edo 6, Osun 4, Anambra 2, Bayelsa 2 da kuma Fitalo mutum 1.

Acewarsa hukumar NCDC yanzu haka adadin wadanda suka kamu da cutar ya kai 179,908, sai dai 166,203 sun warke.

Yayinda mutum 2,195 suka riga mu gidan gaskiya.