Home Labaru Kiwon Lafiya Annoba: Cutar Kwalara Ta Hallaka Mutum 146 a Jihar Kebbi

Annoba: Cutar Kwalara Ta Hallaka Mutum 146 a Jihar Kebbi

172
0

Rahotanni daga Jihar Kebbi sun tabbatar da cewa akalla Mutum 146 sun rasa rayukan su sakamakon annobar cutar kwalara.

Hukumomin Jihar Kebbi sun ce mutanen da suka mutu na daga cikin fiye da mutane 2,000 da suka kamu da cutar.

Sakataren Asibitin Sir Yahaya da ke Birnin Kebbi, Aminu Bunza ya shaida wa manema labarai cewar mutane 2,038 suka harbu da cutar a fadin jihar tun bayan samun ta a Karamar Hukumar Sakaba.

Bunza ya ce bayan barkewar cutar a Dirin Daji dake Karamar Hukumar ta Sakaba yanzu haka cutar amai da gudawan ta yadu zuwa Kananan Hukumomi 20 dake fadin Jihar.

Anata bangaren Hukumar yaki da cututtuka ta kasa NCDC ta ce mutane 816 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar a jihohin Najeriya.

Daga cikin jihohin da cutar ta yi illa akwai Kano wadda ta yi asarar mutane 119 sai Katsina mai mutane 75, Zamfara na da mutane 30 sai kuma Sakkwato mai 23.

Leave a Reply