Home Labaru Badakalar Hushpuppi: Lauyoyin Arewacin Najeriya 13 Sun Yi Tayin Tsayawa Abba Kyari

Badakalar Hushpuppi: Lauyoyin Arewacin Najeriya 13 Sun Yi Tayin Tsayawa Abba Kyari

70
0
ABBA KYARI

Tawagar wasu lauyoyi 13 daga arewacin Najeriya sun yi tayin tsayawa Abba Kyari a tuhumar da ake masa kan rashawa.

Kyari tsohon shugaban tawagar tattara bayanan sirri ta’yan sanda na fuskantar tuhuma ne daga hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka, FBI bisa zargin aika rashawa.

Kafar yada labarai ta Punch ta rawaito kakakin tawagar lauyoyin, Sunusi Bappah Salisu, a wata sanarwa na cewa lauyoyin da suka yi wannan tayin sun fito ne daga yankunan jihohin arewacin Najeriya 19.

A cewarsa, sun fito ne domin bayyana matsayinsu sakamakon kiraye-kirayen da gamayar ƙungiyoyin ƴan arewa suka yi akan lamarin.

Salisu ya ce za su nazarci tuhume-tuhume da ake yi wa Kyari da bukatar miƙa shi ga hukumar FBI da kuma gaskiyar alaƙarsa da fitaccen mai damfarar nan Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi.