Home Coronavirus Majalisar Dattawa Ta Amince Wa Buhari Cin Bashin Naira Biliyan 850

Majalisar Dattawa Ta Amince Wa Buhari Cin Bashin Naira Biliyan 850

349
0
Majalisar Dattawa Ta Amince Wa Buhari Cin Bashin Naira Biliyan 850
Majalisar Dattawa Ta Amince Wa Buhari Cin Bashin Naira Biliyan 850

Majalisar dattawa ta amince wa shugaba Muhammadu Buhari ya karbo rancen kudi naira biliyan 850.

Majalisar ta amince da bukatar ne a zaman da ta yi ranar Talatar da ta gabata, bayan ta dawo daga hutun cutar coronavirus.

Shugaba Buhari dai ya bukaci majalisar ta amince da bukatar sa ta samun rancen daga kasuwar kudi ta cikin gida domin a ba gwamnatin sa damar aiwatar da kasafin shekara ta 2020.

Nijeriya dai ta samu babban gibi daga kudaden da ta ke samu bayan farashin danyen mai ya fadi da kusan kashi 45 cikin 100, lamarin da ya sa gwamnatin Nijeriya ba za ta iya aiwatar da kasafin ta na shekara ta 2020 ba tare da ta nemi taimako ba.

Gwamnatin Nijeriya dai ta tsara kasafin ne a kan dala 57 a duk gangar danyen mai daya, kafin a sake sauya hasashen zuwa dala 30 duk ganga guda.