Home Labaru 23 Sun Warke Daga Coronavirus A Abuja

23 Sun Warke Daga Coronavirus A Abuja

578
0
Mutum 23 ke nan suka warke a Abuja, wadda ita ce ta biyu wurin yawan masu cutar coronavirus a Najeriya.
Mutum 23 ke nan suka warke a Abuja, wadda ita ce ta biyu wurin yawan masu cutar coronavirus a Najeriya.

Yawan mutanen da aka sallama bayan warkewarsu daga cutar coronavirus ya karu zuwa 23 a Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya.

Ministan Abuja Mohammed Musa Bello, ya ce adadin ya karu ne bayan wasu karin mutum 3 sun warke a ranar Laraba 15 ga watan Afrilu, 2020.

Mutum 58 ne suka kamu da cutar ta COVID19, daga lokacin da aka fara samun bullarta a Abuja, wadda ke biye da Legas mai mutum 232.

Amma ba a samu karin masu cutar ba a Abuja a ranar Larabar, a cewar alkaluman da Cibiyar Hana Yaduwar Cututtuka NCDC ta fitar.

Kawo yanzu mutum 407 ne NCDC ta tabbatar sun kamu da cutar a jihohi 20 a Najeriya. Daga adadin 128 sun warke, 12 sun mutu, yayin da 267 ke killace ana duba lafiyarsu.