Home Labaru Kiwon Lafiya Coronavirus: Mutum 5 Sun Karu A Kano

Coronavirus: Mutum 5 Sun Karu A Kano

426
0
Mutum 9 ke nan suka kamu da cutar coronavirus a fadin Jihar Kano.
Wadanda suka kamu da cutar sun yi alaka da mutumin da ya fara harbuwa da ita a jihar Kano

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta tabbatar da karuwar mutum 5 da ke dauke da cutar coronavirus a jihar.

Sanarwar da Ma’aikatar ta fitar a ranar Laraba ta ce sabbin mutum 5 da ke dauke da cutar sun yi alaka da wanda ya fara kamuwa da cutar.

Kawo yanzu mutum 9 ne suka kamu da annobar coronavirus a jihar Kano.

A ranar Laraba, 14 ga watan Afrilun da muke ciki ma an samu karin mutum 1 da ya kamu da cutar, kamar yadda ma’ikatar lafiayr ta tabbtar.

Karuwar masu cutar a jihar ta sa Gamna Abdullahi Ganduje sanya dokar hana zirga-zirga na tsawon sa’a 24 a fadin jihar, a matakin farko.

Gwamnan ya sanar da haka ne a lokacin taron da ya yi da malaman addini kan annobar cutar a ranar Laraba.