Home Labaru Kiwon Lafiya Mutum Na Farko Ya Warke Daga COVID-19 A Kaduna

Mutum Na Farko Ya Warke Daga COVID-19 A Kaduna

418
0
Gwamna Nasir El-Rufa'i na daga cikin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a jihar Kaduna.
Gwamna Nasir El-Rufa'i na daga cikin mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a jihar Kaduna.

An sallami mutum na farko da ya warke daga annobar coronavirus a jihar Kaduna.

Cibiyar Killace Masu Cutar Coronavirus a Jihar Kaduna ta sallami mutumin da ya fara warkewa daga coronavirus ne bayan sakamakon gwajin da aka yi masa har sau biyu ya tabbatar da cewa mutumin ya warke daga cutar.

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar ta ce wanda aka sallaman na daga cikin mutum 6 da suka kamu da cutar a jihar. Ta kuma bayyana fatar ganin sauran mutum 5 da suka kamu da cutar sun warke nan ba da jumawa ba.

Gwmana Nasir El-Rufa’i da wasu manyan jami’an gwamnatinsa na daga cikin mutum 6 da suka harbu da cutar coronavirus a Jihar Kaduna.

Kwamishinar Lafiya ta Jihar Kaduna, Amina Muhammad Baloni, ta kuma yaba wa ma’aikatan lafiya bisa kwarewa da sadaukar da kai da suka nuna a yaki da cutar a jihar.

Baloni ta kuma shawarci jam’an jihar da su guji shiga cinkoson mutane tare da kula da tasfta da sauran matakan kariya, domin ita ce hanya mafi na kauce wa kamuwa da cutar.