Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da kwamitin yaƙi da annobar COVID-19 a fadar sa da ke Abuja.
Mai taimakawa shugaban kasa ta fuskar kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmed ya wallafa haka a shafin sa na Twitter, inda ya ce kwamitin ya yi wa shugaba Buhari bayanin inda aka kwana a yaki da cutar.
Ya ce, kwamitin zai sanar da sabbin matakan yaki da annobar a Nijeriya, inda wa’adin dokar kulle da aka tsawaita a jihar Kano ta tsawon makonni biyu zai kawo ƙarshe, da kuma dokar hana tafiye tafiye tsakanin jihohi bayan ƙara tsawaita sassauta dokar kulle da aka yi a jihohin Legas da Ogun da kuma Abuja.
You must log in to post a comment.