Home Coronavirus Covid-19: NCDC Ta Samar Da Karin Dakunan Gwaji Biyu A Nijeriya

Covid-19: NCDC Ta Samar Da Karin Dakunan Gwaji Biyu A Nijeriya

373
0
Covid-19: NCDC Ta Samar Da Karin Dakunan Gwaji Biyu A Nijeriya
Covid-19: NCDC Ta Samar Da Karin Dakunan Gwaji Biyu A Nijeriya

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce yawan dakunan gwaje-gwajen cutar coronavirus sun karu zuwa 28 a fadin Nijeriya.

NCDC ta bayyana hakan a shafin ta na twitter, tare da cewa an samu karin cibiyoyin gwajin cutar 2 ne a jihohin Katsina da Ogun.

Cibiyar ta kara da cewa, baya ga karin dakunan biyu da aka kaddamar, akwai karin wasu da ake gaf da kammala aikin su a jihohin Gombe da Kwara.

A baya dai, babban daraktan hukumar lafiya ta Duniya WHO Tedros Ghebreyesus, ya ce babu tabbaci a kan adadin masu dauke da cutar COVID-19 a Afrika, saboda karancin wuraren gwaji da nahiyar ke da su.