Home Labaru Kiwon Lafiya Aisha Buhari Ta Bada Talafin Kayan Aiki Da Abinci Domin Yaki Da...

Aisha Buhari Ta Bada Talafin Kayan Aiki Da Abinci Domin Yaki Da Covid-19 A Jihar Nasarawa

549
0
Aisha Buhari Ta Bada Talafin Kayan Aiki Da Abinci Domin Yaki Da Covid-19 A Jihar Nasarawa
Aisha Buhari Ta Bada Talafin Kayan Aiki Da Abinci Domin Yaki Da Covid-19 A Jihar Nasarawa

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bada kwangilar gyara babban asibitin Mararraba Gurku da ke jihar Nasarawa, domin killace wadanda su ka kamu da cutar COVID-19.

Aisha Buhari ta kuma raba kayayyakin abinci ga likitoci da sauran ma’aikatan da su ka sadaukar da rayuwar su domin ceto rayukan al’ummar jihar.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana haka ne a shafin tan a facebook, inda ta ce, an kaddamar da aiki ne a karkashin gidauniyarta mai suna Future Assured.

Daga cikin kayayyakin aikin da aka rabawa ma’aikatan sun hada da rigunan kariya da magungun da masu jinyar cutar COVID-19 su ke bukata domin su murmure.

Bayan kwayoyin rage radadin ciwo, da kara karfin jiki da kwayoyin da ke taimakawa wadanda su ka gaza cin abinci, Aisha Muhammadu Buhari ta raba takunkumin N95 na rufe fuska Kamar yadda Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta bayyana a shafin na ta, ta bada gudumuwar man wanke hannuwa, sannan ta raba abinci a matsayin tallafi ga ma’aikatan lafiya.

Daga cikin kayan abincin da Aisha Buhari ta damkawa gwamnatin jihar Nasarawa sun hada da buhunan shinkafa da dai sauran su.