Home Labaru Bin Doka: Sarkin Musulmi Ya Yi Gargadi Game Da Bijire Wa Umurnin...

Bin Doka: Sarkin Musulmi Ya Yi Gargadi Game Da Bijire Wa Umurnin Kotu

853
0
Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad II
Sarkin Musulmi, Abubakar Sa’ad II

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar II, ya yi gargadi game da rashin bin hukuncin kotu, inda ya ce saba wa umarnin kotu zai janyo rashin aiki da doka a Nijeriya.

Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen wani taro da ya gudana a birnin Abuja, wanda aka yi a kan tasirin Malamai da kungiyoyi wajen kawo zaman lafiya da ci-gaban kasa.

Duk da yak e Sarkin bai kama sunan kowa yayin da yak e jawabin ba, amma ya nuna goyon baya ga tsarin shugabancin kama-kama.

Ya ce bai kamata a rika watsi da dokokin kasa ba, don haka idan kotu ta yanke hukunci a yi gaugawar zartar da shi ba tare da bata lokaci ba, domin babu al’ummar da za ta iya ci-gaba ba tare da bin dokoki ba.

Leave a Reply