Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar II, ya yi gargadi game da rashin bin hukuncin kotu, inda ya ce saba wa umarnin kotu zai janyo rashin aiki da doka a Nijeriya.
Sarkin Musulmin ya bayyana haka ne, yayin da ya ke jawabi a wajen wani taro da ya gudana a birnin Abuja, wanda aka yi a kan tasirin Malamai da kungiyoyi wajen kawo zaman lafiya da ci-gaban kasa.
Duk da yak e Sarkin bai kama sunan kowa yayin da yak e jawabin ba, amma ya nuna goyon baya ga tsarin shugabancin kama-kama.
Ya
ce bai kamata a rika watsi da dokokin kasa ba, don haka idan kotu ta yanke
hukunci a yi gaugawar zartar da shi ba tare da bata lokaci ba, domin babu
al’ummar da za ta iya ci-gaba ba tare da bin dokoki ba.