Home Labaru Tsaro: Za Mu Warware Matsalolin Sojojin Da Ke Yaki A Tafkin Chadi...

Tsaro: Za Mu Warware Matsalolin Sojojin Da Ke Yaki A Tafkin Chadi – Magashi

297
0
Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi
Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi

Ministan Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi Mai ritaya, ya ziyarci garin Monguno domin ganawa da rundunar hadin gwiwa da ke yunkurin kakkabe ‘yan ta’adda a yankin tafkin Chadi da ya kunshi sojojin Nijeriya da na Chadi.

Janar Bashir Magashi, ya yi wata ganawar sirri da rundunar sojin Nijeriya ta tsawon sama da sa’o’i uku a garin Monguno da ke jihar Borno.

Yayin da ya ke yi wa sojojin hadin gwiwar bayani, Magashi ya ce aikin sojoji da sauran jami’an tsaro ya na da muhimmanci, domin ta dalilin su ne sauran mutane ke iya gudanar da ayyukan su.

Ya ce aikin sojojin ya hada da kare mutuncin kasa yadda ya kamata, da kuma taimaka wa fararen hula wajen maido da doka da oda.

Janar Magashi, ya ce Shugaba Buhari ya bukaci ya mika sakon fatan alheri da kuma goyon bayan sa gare su, game da irin ayyukan da sojojin ke yi a yankin arewa maso gabashin Nijeriya.