Tsohon ministan sufurun jiragen sama a Nijeriya, kuma jigo a jam’iyyar PDP Femi Fani Kayode, ya ce ya gwammace rai ya yi halin shi da ya koma jam’iyyar APC.
Fani Kayode ya wallafa hakan ne a shafin sa na Twitter, inda ya ce masu cewa ya bar jam’iyyar PDP zuwa APC karya ce tsagwaron ta, ya na mai bayyana APC a matsayin jam’iyyar Almajirai.
Wannan
dai ya na zuwa ne, kwanaki kadan bayan wani rahoto da aka yada a kafafen sada
zumunta cewa Femi Kayode ya koma jam’iyyar APC.