Home Labaru Lakabi: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Fitar Da Sabon Hoto Da Suna A...

Lakabi: Shugaban Majalisar Dattawa Ya Fitar Da Sabon Hoto Da Suna A Hukumance

639
0
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa
Sanata Ahmed Lawan, Shugaban Majalisar Dattawa

Ofishin shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmda Lawan, ya fitar da hoton sa, da kuma sunan da za rika amfani da su a hukumance.

A cikin wata sanarwar yanar gizo da ofishin ya aike wa kafafen yada labarai, an bayyana cewa, tare da sakon akwai hoton mai girma shugaban majalisar dattawa da za rika amfani da su a hukumance.

Sakon ya cigaba da cewa, shugaban majlisar dattawa ya zabi rika kiran sa Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, Ph.D, CON, kamar yadda ya ke a jikin hoton.