Home Coronavirus Barna: COVID-19 Ta Kashe Mutane 193 Cikin Kwanaki 20 A Najeriya

Barna: COVID-19 Ta Kashe Mutane 193 Cikin Kwanaki 20 A Najeriya

185
0

Rahotanni sun ce annobar Coronavirus na ci gaba da barna ta hanyar karuwar yawan masu dauke da ita da kuma wadanda take kashewa tun farkon sabuwar shekarar 2020 kamar yadda aka gano.

Alkaluman da aka tattara daga Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC sun nuna cewa mutane 193 ne suka mutu sanadiyyar cutar daga cikin kwanaki 20, tsakanin hudu da kuma 24 ga watan Janairun 2021.

Rahoton ya ce ya zuwa ranar Laraba, akalla mutane dubu 126, da 160 aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya, dubu 24 da 251 daga cikin su har yanzu suna dauke da ita, yayin da dubu 1 da 544 kuma suka mutu.

A ranar litinin gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa sabon nau’in cutar wanda ake wa lakabi da B117 da aka samo daga kasar Burtaniya ya bulla a Najeriya.

Da yake jawabi yayin taron Kwamitin Kar-ta-kwana da Gwamnatin Tarayya ta Kafa don Yaki da Cutar kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya ce masana ilimin kimiyya sun dukufa wajen nazarin cutar.

Ya kuma koka kan yadda ya ce ana kara samun masu dauke da cutar a cikin ’yan makonnin nan, musamman ta la’akari da rahoton alkaluman da suke fita a kullum.