Home Labaru Zaman Lafiya: Shugabanin Kasashen Yankin Afrika Ta Tsakiya Na Taro A Angola

Zaman Lafiya: Shugabanin Kasashen Yankin Afrika Ta Tsakiya Na Taro A Angola

209
0

Shugabanin kasashen yankin Afrika ta tsakiya na gudanar da taron su a Luanda dake babban birnin kasar Angola da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika tun bayan da sojojin tareda hadin gwuiwar dakarun kasashen waje suka murkushe yan tawayen da suka yi kokarin sa kai zuwa babban birnin kasar Bangui.

Taron na Angola na zuwa ne a wani lokaci da hukumar kula da ‘yan cin rani ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce zuwa yanzu mutane fiye da dubu dari 2 rikici ya raba da muhallansu a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya ciki har da wasu fiye da dubu 100 a cikin kasar yayinda makamancin adadin suka tsere makwabtan kasashen.

Alkaluman na Majalisar Dinkin Duniyar na zuwa dai dai lokacin da wasu bayanai ke cewa yanzu haka anfara wani wani zaman tattaunawa a Angola don kawo karshen rikicin Afrika ta tsakiyan da ke ci gaba da tsananta.