Home Labaru Ilimi Bincike: Fitattun ‘Yan Najeriya Na Amfani Da Makarantun Birtaniya Wajen Sace Dukiyar...

Bincike: Fitattun ‘Yan Najeriya Na Amfani Da Makarantun Birtaniya Wajen Sace Dukiyar Talakawa

203
0

Wata Gidauniyar zaman lafiyar duniya ta Amurka da ake kira ‘Carnegie Endowment for International Peace’ ta zargi manyan ‘yan siyasar Najeriya da amfani da makarantun Ingila wajen sace dukiyar talakawa.

Rahotan kungiyar yace wadannan ‘Yan siyasa na amfani da shirin kai daliban su kasar ne da zummar yin karatu, amma kuma a karkashin kasa sai su dinga amfani da shirin suna kwashe kudaden jama’a.

Binciken da Mathew Page ya gudanar a madadin kungiyar da taimakon gwamnatin Birtaniya da Jakadan Birtaniya dake Najeriya yace an kaddamar da shi ne domin gano illar da irin wadannan kudade da ake shiga da su Birtaniya daga Afirka ta Yamma ke yiwa kasar, domin daukar matakan da suka dace.

Jakadiyar Birtaniya a Najeriya Catriona Laing tace daukar matakan dakile cin hanci da rashawa a Najeriya ya zama tilas domin samarwa kasar tsaro da cigaba musamman wajen yaki da talauci da kuma rashin daidaito a tsakanin al’umma.

Laing tace suna aiki tare da hukumomin Najeriya domin shawo kan cin hanci da rashawa da kuma dakile halarta kudaden haramun tare da hukumomin kasar.