Babban Alkalin kotun tarayya da ke Minna, mai shari’a Aminu Aliyu, ya bada umurnin kama tsohon gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu da Umar Nasko.
Mai shari’a Aliyu ya kuma janye belin da mai shari’a Yellim Bogoro ya ba Aliyu da Nasko, saboda rashin bayyanar su a kotu domin ci-gaba da sauraron shari’ar da ake musu.
Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya ruwaito cewa, kotu ta bukaci Aliyu da Nasko su gurfana a gaban ta a ranar Alhamis ne, domin sake fara sauraron shari’ar tuhumar da ake musu na damfarar naira biliyan 1 da miliyan 9 da aka maida zuwa kotun da mai’shari’a Aliyu ke jagoran ta.
Lauyan tsohon Gwamna Aliyu Olajide Ayodele, ya aike wa kotu da wasika, inda ya bukaci a dage cigaba da sauraron karar, wanda daga karshe aka dage ta zuwa ranar 27 ga watan Mayu na shekara ta 2019.