Home Labaru Kudin Nome Ciyawa: Babachir Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Saboda Hujjojin...

Kudin Nome Ciyawa: Babachir Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Saboda Hujjojin Da EFCC Ta Gabatar A Kotu

325
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gabatar wa babbar kotun tarayya da ke Maitama Abuja da wata shaidar kara da ta shigar da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal.

EFCC ta gurfanar da Babachir da Hamidu David da Suleiman Abubakar da Apeh John Monday da kamfanoni biyu Rolavision Engineering Ltd da Josmon Technologies Ltd a gaban Alkali Jude Okeke kan tuhumar su da aikata laifuka 10 da su8ka jibanci satar naira miliyan 500.

A zaman farko na sauraron karar, hukumar EFCC ta gabatar wa kotu da Hamza Adamu Buwai, wanda ma’aikaci ne a ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, kuma shine jami’i mai kula da kudi na kwamitin shugaban kasa mai kula da Arewa maso gabas.

Hamza ya shaida ma kotu cewa, shine ya ke kula da biyan kudaden ‘yan kwangilar da suka yi aiki karkashin kwamitin, saboda haka shine ya biya kamfanin Rolavision naira miliyan 225 daga cikin kudin kwangilar naira miliyan 272.

Sai dai lauyoyin masu kara da wanda ake kara sun yi ta kai ruwa rana a gaban kotu, a kan sahihanci ko akasin haka na takardun biyan kudin da gwamnati ta yi wa kamfanonin biyu, wanda hakan yasa Alkalin kotun ya dage yanke hukuncin zuwa ranar 17 da 18 ga watan Yuni.