Home Labaru Zaman Lafiya: Kungiyar Generation For Peace Ta Fara Amfani Da Hanyoyin Kirkire-Kirkiren...

Zaman Lafiya: Kungiyar Generation For Peace Ta Fara Amfani Da Hanyoyin Kirkire-Kirkiren Kayayyakin Al’udu

305
0

Wata kungiyar tabbatar da zaman lafiya a cikin alumma mai suna Generation For Peace ta fara amfani da hanyoyin kirkiran kayayyakin al’adu gargajiya wajen tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.
Mataimakiyar shugabar kungiyar Jalila Tabidoyon ta bayyana haka a lokacin da kungiyar ta shiryawa alummar guda 60 wani taro a Kaduna.
Jalila, ta ce kungiyar ta zabo hanyoyin kirkire-kirkire ne domin tabbatar da cewar hanyoyin al’adu nada rawar da za su iya takawa wajen tabbatar da zaman lafiya.
Mataimakiyar shugaban kungiyar ta koka akan yadda aka sami karancin fitowar alumma a wannan karon, inda ta bukaci ganin matasa su kara azama wajen tabbatar da zaman lafiya.
Daya daga cikin halarta taron Hajiya Lami Umar ta ja hankalin matasa su fara amfani da yarensu da kuma kabilarsu wajen kara bunkasa zaman lafiya a Najeriya.
Daga karshe ta bukaci matasa akowane lokaci su rika amfani da hanyyoyin yada al’adu wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin alumma, saboda sai da zaman lafiya ake samun ci gaba.