Home Coronavirus Babu Kudin Sayo Abinci Dole Manoma Su Koma Noma-Buhari

Babu Kudin Sayo Abinci Dole Manoma Su Koma Noma-Buhari

1557
0
Babu Kudi Sayo Abinci Dole Manoma Su Koma Noma-Buhari
Babu Kudi Sayo Abinci Dole Manoma Su Koma Noma-Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci manoman Nijeriya su zage damtse wajen noma a wannan shekarar domin gwamnati ba ta da kudin shigo da abinci daga kasashen ketare.

Buhari ya bayyana haka ga manema labarai jim kadan bayan ya kammala sallar Idi a fadar sa da ke Abuja, sannan ya yi wa manoman fatan samu damina mai albarka.

Idan dai ba a manta ba, tun kafin barkewar annobar coronavirus, Nijeriya ta rufe iyakokin ta tudu domin hana shigo da kayan abinci irin su shinkafa da Kaji da kuma man fetur.

Haka kuma, shugaba Buhari ya gargadi ‘yan Nijeriya su rika bin dokokin ma’aikatan kiwon Lafiya game da annobar Coronavirus, domin cutar ta dagula komai a kasashe masu tasowa da kashen da suka cigaba.

Ko a makon daya gabata ma, ministar kudi Zainab Samsuna Ahmed ta ce babu makawa sai Nijeriya ta fada cikin halin tabarbarewar tattalin arziki, sakamakon yadda kasar ta dogara da man fetur, kuma farashin sa ya fadi kasar warwas a dalilin  cutar Coronavirus.