Home Labaru Atiku Ya Taya Musulamai Murnar Bikin Sallah

Atiku Ya Taya Musulamai Murnar Bikin Sallah

341
0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya taya Musulmin Nijeriya da na duniya murnar bikin karamar Sallah.

Atiku Abubakar ya kuma ya taya Musulmi juyayin yin bikin Sallar cikin wai ni yanayi da ba su saba gani ba, sabanin yadda su ka saba yin Sallar cikin farin ciki da walwala.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafin sa na tuwita, inda ya kara da cewa  annobar corona wata jarrabawa ce daga Allah.

Atiku ya kuma yi kira ga shugabanni su nuna sadaukarwa a wannan lokaci, kuma ya kamata su jingine rayuwar kawa da jin dadi domin nuna tausayawa ga al’umma.

Haka kuma, ya bukaci shugabanni a fadin duniya su kasance masu koyi da kyawawan halaye irin na Annabi Muhammad S.A.W, da sauran halifofin sa da su ka nuna sadaukarwa yayin da su ke rike da shugabanci.

A karshe Atiku ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su guji cunkusuwa a wajen guda, sannan su yawaita yawan wanke hannu da sabulu, da kuma yin biyayya ga sauran matakan kare kai da kamuwa da  cutar Coronavirus.