Home Coronavirus Mutum 10 ‘Yan Gida Daya Sun Kamu Da Cutar Covid-19 A Kaduna

Mutum 10 ‘Yan Gida Daya Sun Kamu Da Cutar Covid-19 A Kaduna

537
0
Mutum 10 ‘Yan Gida Daya Sun Kamu Da Cutar Covid-Mutum 10 ‘Yan Gida Daya Sun Kamu Da Cutar Covid-19 A Kaduna19 A Kaduna
Mutum 10 ‘Yan Gida Daya Sun Kamu Da Cutar Covid-19 A Kaduna

An samu karin mutane 10 ‘yan gida daya da suka kamu da annobar Coronavirus a jihar Kaduna.

Gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai, tare da cewa an samu karin wasu mutane 18 da suka kamu da cutar ranar Alhamis, 14 daga cikin su sun fito ne daga karamar hukumar Kaduna ta Arewa, biyu daga Zaria, kananan hukumomin Chikun da Sabon Gari na da mutum guda-guda.

Idan dai ba a manta ba, gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya ce da kan sa zai fita domin tsare iyakar Kaduna da Kano a ranar Sallah, domin dakile yaduwar cutar Coronavirus.

Haka kuma, gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar zaman gida inda ta ware ranakun Laraba da Alhamis domin mutane su fita don siya kayayyakin abinci