Shugabar Kotun Daukaka Kararrakin Zaben Shugaban Kasa Zainab Bulkachuwa, ta yi barazanar yin maganin lauyoyi, da masu kai korafe-korafe da ’yan jarida da aka kama su na sharhi a kan duk wata karar da ke a gaban kotun.
Bulkachuwa ta ce, duk lauyan da aka kama ya na sharhin kararrakin a kafafen yada labarai bayan zaman kotu, to Kotun Daukaka Kara za ta yi maganin sa.
Mai shari’a Bulkacuwa ta yi gargadin ne, yayin da ta kaddamar da fara zaman kotun a ranar Labarar da ta gabata a Abuja.
Ta ce irin wadannan rubuce-rubuce da sharhin su na kawo wa kotu cikas da kuma tarnaki ga yanke hukunci, sannan ya na jefa waswasi ga jama’a a kan hukuncin da kotu za ta yanke.
Bulkacuwa ta kara da cewa, sun sha ganin yadda wasu ke rika yin rubuce-rubuce a kafafen sadarwa na zamani, ko surutai a gidajen radiyo da talbijin a kan wasu shari’o’in da ke gaban kotu da ba a riga an yanke hukunci ba.
A karshe ta ce wannan gargadin ya shafi hatta jam’iyyun siyasa da magoya bayan su.
You must log in to post a comment.