Gwamman jihar Katsina Aminu Bello Masari, ya ce babu makawa za a samu karancin abinci a yankuna da ke fama da ta’addancin ‘yan bindiga.
Wurare da dama dai na ci-gaba da fargabar yadda rashin tsaro ke barazana ga noma a yankunan da ke fama da garkuwa da mutane a Nijeriya,
Gwamna Masari ya bayyan haka ne, yayin wata hira da ya yi da manema labarai.
Masari ya tabo batuwa da dama da su ka shafi tsaro a yankunan jihar sa da ma na makwabta, ciki har da batun irin kokarin da gwamnatocin yankunan ke yi na kawo karshen hare-hare da ma satar mutane da ake yi.
You must log in to post a comment.