Home Home Atiku Ya Roƙi CBN Ya Ƙara Wa’adin Daina Karɓar Tsofaffin Kuɗi

Atiku Ya Roƙi CBN Ya Ƙara Wa’adin Daina Karɓar Tsofaffin Kuɗi

33
0
Ɗan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar PDP Atiku Abubakar, ya yi kira ga Babban Bankin Nijeriya ya ƙara wa'adin daina karɓar tsofaffin kuɗin da aka sauya.

Ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya yi kira ga Babban Bankin Nijeriya ya ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin kuɗin da aka sauya.

Atiku Abubakar, ya ce idan aka yi duba da halin matsin da al’umma ke ciki, ya kamata a ƙara wa’adin zuwa wani ɗan lokaci.

Ya ce sauya fasalin kuɗi ba wani sabon abu ba ne a fadin duniya, sai dai wa’adin da aka tsaida na ranar 31 ga watan Janairu zai jefa mutane cikin mawuyacin hali.

Atiku ya kara da cewa, da yawan ‘yan Najeriya musamman manoma da masu sana’ar hannu da mazauna ƙauyuka ba su da asusun banki, don haka lokacin da aka kayyade na daina karbar tsofaffin kuɗin ba mai yiwuwa ba ne.