Home Home An Kama Mutum 8 Kan Zargin Tayar Da Tarzoma Yayin Ziyarar Buhari...

An Kama Mutum 8 Kan Zargin Tayar Da Tarzoma Yayin Ziyarar Buhari A Katsina

22
0
 ‘Yan sanda sun kama wasu mutane takwas da ake zargi da tada tarzoma yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara Jihar Katsina.

 ‘Yan sanda sun kama wasu mutane takwas da ake zargi da tada tarzoma yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara Jihar Katsina.

Shugaba Buhari dai ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu birnin Katsina, inda ya kaddamar da ayyuka da dama.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na Jihar Katsina Gambo Isah, ya ce bayan shugaban kasa ya kaddamar da aikin gadar kasa ta Kofar-Kaura, an samu labarin cewa wasu bata-gari daga Sabuwar Unguwa sun shiga hannu bisa zargin su ta tada tarzoma.

Ya ce wani bincike da ‘yan sanda su ka gudanar ya nuna cewa, bata gari sun yi amfani da yara ne wajen haddasa husuma a yankin ta hanyar jifar tawagar ‘yan sanda.

Gambo Isah ya cigaba da cewa, wadanda aka kama su na taimaka wa ‘yan sanda a binciken da su ke gudanarwa a yanzu.