Home Labaru Arewa Maso Gabas: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Aikin Gadar Ibbi

Arewa Maso Gabas: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Aikin Gadar Ibbi

1199
0

Gwamnatin tarayya ta fara aikin gina gadar da za ta hada yankin arewa maso gabashin Najeriya da babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun ce tuni ma’aikata da kayayyakin aiki suka fara isa wuraren da za a gudanar da aikin wanda ake gani zai saukaka zirga-zirga a tsakanin al’umma.

An yiwa kayayyakin sansani ne a garin Ibbi dake jihar Taraba  ta inda ake sa ran gadar za ta ratsa kogin Benue.

Mazauna yankin dai sun nuna farin cikin su da isowar kayayyakin aikin da kuma ma’aikatan, sakamakon yadda suka dade suna neman gwamnatin tarayya ta gudanar da wannan aiki.