Home Labaru Almundahana: Hukumar ICPC Ta Rufe Asusun Ajiyar Banki Na Yari

Almundahana: Hukumar ICPC Ta Rufe Asusun Ajiyar Banki Na Yari

248
0
Kotu Ta Hana Efcc Kwace Kadarorin Yari
Kotu Ta Hana Efcc Kwace Kadarorin Yari

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran wasu laifukka makamantan haka ICPC ta samu amincewar babbar kotun tarayya dake Abuja na rufe asusun ajiyar bankin tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’azeez Yari.

Mai magana da yawun hukumar ta ICPC Rasheedat Okoduwa

Mai magana da yawun hukumar ta ICPC Rasheedat Okoduwa, ta tabbatar da haka, ta ce Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya yanke hukuncin amincewa da rufe asusun na bankuna 2 wanda a cikin su akwai sama da dala dubu dari 6 da 69 da kuma Nair milliyan 24.

Ta ce ana zargin tsohon gwamnan ne da karkatar da kudaden zuwa asusun ajiyarsa da kuma na wasu kamfanoni mallakinsa.

Alkalin ya kuma umurci hukumar da ta buga hukuncin da kotun ta dauka na rufe asusun ajiyar bankin tsohon gwamnan da kamfanoninsa a jaridar kasa a cikin kwanaki 14 masu zuwa.

Ta kuma kara da cewa kotun ta umurci wadanda abin ya shafa da su bayyana dalilan da za su sa ba za a kwace kudaden a ba gwamnatin tarayya baki daya ba.