Home Labaru Tsaro Duba Lafiya: Mun Maido Da Zakzaky Gida Saboda Yana Neman Mafaka –...

Duba Lafiya: Mun Maido Da Zakzaky Gida Saboda Yana Neman Mafaka – Gwamnati

291
0

Gwamnatin tarayya ta ce ta maido da shugaban haramtacciyar kungiyar IMN Ibrahim Zakzaky Najeriya ne saboda yana neman mafaka a wata kasa a yankin Asia.

Babbar sakatariyar ma’aikatar kula da harkokin yada labarai da al’adu Grace Isu Gekpe ta tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ta fitar.

Babbar sakatariyar ma’aikatar kula da harkokin Grace Isu Gekpe

Ta ce Zakzaky na kokarin rage kimar da Najeriya ke da shi a idon duniya ta hanyar kunyatar da kasar da wasu dabi’unsa marasa kyau.

Grace, ta ce abin da ya yi a India ba wai abu ne da zai batawa Najeriya suna ita kadai ba, har da kasar India. 

Ta kara da cewa akwai wasu halayya da Zakzaky ya yi a kasar wanda ya sabawa aiki da kuma huldar jakadancin kasashe.

Sannan ana zargin Al-Zakzaky da tattaunawa da wasu kungiyoyin Shi’a da kungiyoyin kare hakkin Musulmai, tare da fada musu wasu karairayi, domin su bashi mafaka a kasashen su.

Sannan sanarwar ta zargi uwar gidan Zakzaky da kokarin bata jami’an tsaron India da na Najeriya ta hanyar yin karyar cewa sun kashe mata ‘ya’ya da danganta su da sauran muggan ayyuka.

A ranar Juma’a 16 ga watan Agusta ne dai Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya isa Najeriya bayan yunkurin kula da lafiyarsa da mai dakinsa Zeenat ya ci tura a kasar Indiya