
Hukumar ɗakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 110 da suka kamu da cutar korona a Najeriya.
Alƙalumman sun nuna mutum 27 suka kamu da cutar a jihar Imo sai a jihar Katsina da aka samu mutum 23 a ranar Lahadi.
Sauran sun hada da jihar Rivers inda aka samu mutum 20, sai jihar Ondo mai mutum 11.
Hukumar tace a jihar Kaduna ma an samu ƙarin mutum 9 da suka kamu da cutar.
Ya zuwa dai yanzu dai jimillar mutum 214,092 suka kamu da cutar a Najeriya yayinda 207,254 suka warke mutum 2,976 suka rasa rayukan su.
You must log in to post a comment.