Home Labaru Yaki Da Ta’addanci: Jirgin Yakin Super Tucano Ya Kashe Mayakan Iswap 26...

Yaki Da Ta’addanci: Jirgin Yakin Super Tucano Ya Kashe Mayakan Iswap 26 A Jihar Borno

110
0
Sabon jirgin yaƙin Super Tucano ya kai hari a maboyar mayaƙan ISWAP tare da lalata motocinsu a Gajiram da ke jihar Borno.

Sabon jirgin yaƙin Super Tucano ya kai hari a maboyar mayaƙan ISWAP tare da lalata motocinsu a Gajiram da ke jihar Borno.

Kafar yaɗa labaran PRNigeria ta ce masu tayar da ƙayar bayan sun shiga garin ne a cikin motocin yaƙi da zummar kai hari, sai jirgin yaƙin ya isa wajen.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ƙwato makamai da dama a yayin da dakarun sama da na ƙasa suka fatattaki mayaƙan.

PRNigeria ta ce wani jami’in leƙen asiri na soja ya ce a ƙalla an ga gawarwarki 26 na mayaƙan bayan hare-haren saman.

A watan Yuli ne Najeriya ta karɓi jiragen yaƙi samfurin Super Tucano da ta saya daga Amurka da nufin magance matsalar tsaro.

Jirgin Super Tucano yana aikin tattara bayanan sirri da sa ido da kai harin sama da ƙasa, kuma ƙwararu sun ce zai taimaka wa ƙasar yin yaƙi da ta’addanci.

Leave a Reply