Home Labarai Afghanistan: Gwamnatin Taliban Za Ta Fara Tattaunawa Da Amurka

Afghanistan: Gwamnatin Taliban Za Ta Fara Tattaunawa Da Amurka

33
0
A yau litini ne ake sa ran Amurka da Taliban za su fara zama karo na biyu domin tattaunawa tun bayan da kungiyar ta kwace iko a kasar Afghanistan.

A yau litini ne ake sa ran Amurka da Taliban za su fara zama karo na biyu domin tattaunawa tun bayan da kungiyar ta kwace iko a kasar Afghanistan.

Kafafen watsa labaran cikin kasar ta Afghanistan sun ce za a yi ganawar ne a kasar Qatar, abin da ke nuni da irin zakuwar da al’ummar kasar ke yi na ganin an yi wannan tattaunawa.

Amurka ta ce taron da aka shirya yi na tsawon mako biyu zai kare muradunta ne da suka hada da yaki da ta’adanci da kuma batun tattalin arzikin kasar ta Afghanistan wanda ya shiga wani hali.